Charming Romantic Encounter at Busy African Marketplace
african marketplace romance · accidental encounter scene · dropped books romance · warm natural sunlight
Nabil da Nabila – Épisode 1 A wani gari mai cike da natsuwa da walwala, akwai wani saurayi mai suna Nabil. Nabil saurayi ne mai hankali, kamun kai da tausayi. Kowa a unguwa yana girmama shi saboda halayensa. A gefe guda kuma akwai wata kyakkyawar budurwa mai suna Nabila. Nabila tana da kyau, nutsuwa da tarbiyya. Duk wanda ya san ta, ya san tana da zuciya mai kyau. Wata rana a kasuwa, Nabil ya je sayayya. Yana cikin tafiya sai ya yi karo da Nabila ba tare da ya sani ba, littattafan da ke hannunta suka zube ƙasa. Nabil ya durƙusa ya taimaka mata tattarawa yana cewa: "Yi haƙuri ban ganki ba." Nabila ta kalle shi cikin murmushi ta ce: "Ba komai, hakan yakan faru." Tun daga wannan lokaci, zuciyar Nabil ta fara bugawa da sauri. Bai taɓa ganin budurwa mai nutsuwa da kyau irin Nabila ba. Shi ma Nabila ta ji wani irin abu a zuciyarta, amma ta ɓoye. Da suka rabu, Nabil ya tsaya yana kallonta har ta ɓace daga gani, sannan ya ce a ransa: "Wacece wannan? Kuma me ya sa zuciyata ta kasa mantawa da ita?" A nan ne labarin soyayyar Nabil da Nabila ya fara... Composition optimized for a 1:1 aspect ratio.